<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><title>Ruhun Iko, Zo Gare Mu LW201</title>
<lyrics>[V1]
 1)Ruhun iko, zo gare mu,
 Mun ga kasawarmu yau.
 Rashin jinƙai, rashin ƙauna
 Rashin musun kanmu ma.

[V2]
 KORUS
 Sai ka zo, ka tsarkake mu
 Daga dukan kasawa.
 Muna jira, muna jira,
 Tsarkake mu duk yanzu.

[V3]
 2) Ruhun sani, zo gare mu,
 Akwai duhu cikinmu.
 Sanasshe mu, koya mana
 Hanyar tsarkakewar rai.
 Korus

[V4]
 3) Ruhun wuta, zo gare mu,
 Kone duk muguntarmu
 Har mu zama mutanenka
 Cikin dukan gaskiya.
 Korus

[V5]
 4) Ruhun haske da addu'a,
 Bi da mu, ka ƙarfafa.
 Muna bege, muna bege
 Har mu sami nasara.
 Korus

[V6]
 5) Ruhun ƙauna, zo gare mu,
 Sai ka yafe mu yanzu.
 Muna jira, muna kuka,
 Amsa dai addu'armu.
 Korus

[V7]
 6) Ƴanuwa, ku yafa Yesu,
 Yafa sabon hali kuwa.
 Yafa kuma zuciyar tausayi,
 Ladabi da jurewa.
 Korus

[V8]
 7) Ruhun Kristi, ni na gode,
 Kana nan a zuclya,
 Mallake ni, mallake ni
 Daga yau har abada.
 Korus</lyrics>
<hymn_number>201</hymn_number>
</song>